Kasashen G5 Na Sahel Na Taron Gaggawa Kan Matsalar Tsaro
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i17379-kasashen_g5_na_sahel_na_taron_gaggawa_kan_matsalar_tsaro
Yau Litinin shugabannin kasashen G5 na Sahel na wani taron gaggawa kan matsalar tsaro a Bamako babban birnin kasar Mali.
(last modified 2018-08-22T06:59:38+00:00 )
Feb 06, 2017 07:40 UTC
  • Kasashen G5 Na Sahel Na Taron Gaggawa Kan Matsalar Tsaro

Yau Litinin shugabannin kasashen G5 na Sahel na wani taron gaggawa kan matsalar tsaro a Bamako babban birnin kasar Mali.

Kasashen da suka hada da Mali, Nijar, Burkina Fasao, Chadi da kuma Mauritania zasu maida hankali kan matsalar tsaro a kasar ta Mali da kuma illarsa a yankin na Sahel.

Hakazalika kasashen zasu duba yadda mayakan jihadi ke fadada ayyukansu a yankin a 'yan shekarun baya bayan nan, wanda ka kasashen ke hasashen kafa wata rundinar hadin gwiwa domin yin sintiri a yankin na Sahel.

Daga cikin kasahen membobin kungiyar da akwai dai wadanda suka taba fuskantar hare haren mayakan jihadin wadanda suka hada da Mali, da Burkina Faso da Nijar har ma da makofcciyarsu Ivory Coast.