Somaliya: Za A yi Zaben Shugaban Kasa A Yau Laraba
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i17431-somaliya_za_a_yi_zaben_shugaban_kasa_a_yau_laraba
Bayan Jinkiri na wasu lokuta za a yi zaben shugaban kasar Somaliya a yau laraba da 'yan takara 22 su ke gogayya da juna.
(last modified 2019-01-16T07:30:45+00:00 )
Feb 08, 2017 06:34 UTC
  • Somaliya:  Za A yi Zaben Shugaban Kasa A Yau Laraba

Bayan Jinkiri na wasu lokuta za a yi zaben shugaban kasar Somaliya a yau laraba da 'yan takara 22 su ke gogayya da juna.

Bayan Jinkiri na wasu lokuta za a yi zaben shugaban kasar Somaliya a yau laraba da 'yan takara 22 su ke gogayya da juna.

Kamfanin dillancin labarun Faransa ya ambato cewa; Zaben na yau wanda baya ga na shugaban kasa, da akwai na 'yan majalisun dokoki da na dattijai. Majalisar dokokin dai tana da kujeru 275 sai kuma majalisar dattaijai mai kujeru 54.

Fitattun 'yan takarar shugaban kasar dai sun hada da shugaba mai ci a yanzu, Hasan Sheikh Mahmud da Pira minista  Umar Abdurrashid Ali Sharmaraki, sai tsohon shugaban kasaSharif Sheikh Ahmad.

Ana hasashen cewa a zagaye na farko,babu daya daga cikin 'yan takarar da zai iya lashe kaso daya bisa uku, 1%3 na jumillar kuri'un da za a kada, da shi ne zai bada damar lashewa.