Shugaban Kamaru Ya Jinjinawa Tawagar Kwallon Kafar Kasarsa
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i17465-shugaban_kamaru_ya_jinjinawa_tawagar_kwallon_kafar_kasarsa
Shugaban kasar Kamaru Paul Biya, ya jinjinawa kwazon da tawagar kwallon kafar kasarsa ta nuna, na lashe kofin gasar kwallon kafar nahiyar Afirka na bana wadda ta gudana a kasar Gabon.
(last modified 2018-08-22T06:59:39+00:00 )
Feb 09, 2017 02:19 UTC
  • Shugaban Kamaru Ya Jinjinawa Tawagar Kwallon Kafar Kasarsa

Shugaban kasar Kamaru Paul Biya, ya jinjinawa kwazon da tawagar kwallon kafar kasarsa ta nuna, na lashe kofin gasar kwallon kafar nahiyar Afirka na bana wadda ta gudana a kasar Gabon.

Kamaru ta doke Masar a wasan karshe da suka buga ranar Lahadi da ci 2 da 1, inda ta dauki kofin wannan gasa a karo na 5.

Kafin fara gasar dai ba a zata Kamaru za ta taka wata rawar gani ba, kasancewar a gasar shekarar 2015 wadda ta gudana a Equatorial Guinea, an cire ta tun a wasannin rukuni.

Da yake yabawa tawagar 'yan wasan da jami'an su, yayin wata liyafa da aka shirya a fadar gwamnatin kasar a jiya Laraba, shugaba Biya ya ce, kasarsa ta farfado a fannin kwallon kafa. Ya ce, shi da al'ummar kasarsa na matukar alfahari da nasarar kungiyar.

A watan Disambar bara ma dai shugaba Biya ya furta makamantan wadannan kalamai, lokacin da kungiyar kwallon kafar mata ta kasar ta zo na biyu a gasar nahiyar ajin mata karo na 1.