Afrika Ta Kudu : An Jibge Sojoji Gabanin Jawabin Zuma A Majalisa
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i17473-afrika_ta_kudu_an_jibge_sojoji_gabanin_jawabin_zuma_a_majalisa
Rahotanni daga Afrika ta Kudu na cewa an jibge dariruwan sojoji a gaban majalisar dokokin kasar a gabanin jawabin da shugaba Jacob Zuma zai yi a majalisar dokokin kasar.
(last modified 2018-08-22T06:59:39+00:00 )
Feb 09, 2017 02:21 UTC
  • Afrika Ta Kudu : An Jibge Sojoji Gabanin Jawabin Zuma A Majalisa

Rahotanni daga Afrika ta Kudu na cewa an jibge dariruwan sojoji a gaban majalisar dokokin kasar a gabanin jawabin da shugaba Jacob Zuma zai yi a majalisar dokokin kasar.

Yau ne dai Mista Zuma dake shan suka daga bangaren 'yan adawa zai yi jawabinsa na shekara shekara a majalisar sai dai gwamnatin kasar ta ce ta jibge dakaru sama da 400 domin tabbatar da tsaro da kuma kaucewa duk wata irin yatsaniya.

Tuni babbar jam'iyyar adawa ta kasar (DA) ta kalubanlanci matakin jibge dakarun, wanda ta ce ya sabawa kundin tsarin mulkin kasar, wanda kuma a cewarta ya nuna yadda bangaren masu mulkin ke shirin zuwa a fusace a majalisar.

A shekrun biyu da suka gabata nan Shugaba Zuma na fuskantar ihu da zanga-zanga a ciki da waje a duk lokacin da yazo yin jawabi a majalisar dokokin kasar.

A shekara 2015 data gabata 'yan majalisar EFF ne suka hana Mista Zuma yin jawabi a majalisar, kafin daga bisani 'yan sanda suyi waje dasu.