An yawa da Zaben kasar Somaliya
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i17521-an_yawa_da_zaben_kasar_somaliya
MDD da wasu Kasashe sun yi maraba da sakamakon zaben Shugaban kasar Somaliya
(last modified 2019-01-16T07:30:45+00:00 )
Feb 10, 2017 15:58 UTC
  • An yawa da Zaben kasar Somaliya

MDD da wasu Kasashe sun yi maraba da sakamakon zaben Shugaban kasar Somaliya

A cikin wani sakon taya murka da suka aikewa kasar Somaliya, MDD, Kungiyar Tarayyar Turai, kasashen Ethiopia, Italiya, Suizilland, Birtaniya da Amurka sun yi marhabin da Sakamakon zaben kasar sannan sun yi taya Sabon Shugaban kasar Muhamad Abdull...Farmajo murna.sannan kuma sun jinjinawa Shugaban kasar mai barin gado Hasan Shekh Muhamad tare da Gwamnatinsa kan irin kokarin da suka yi a shekaru hudun da suka gabata

Duk da cewa an yi ta samun jinkirin gudanar da zaben, sanadiyar matsalar rashin tsaro a kasar, daga karshe a ranar Larabar da ta gabata an gudanar da zaben inda Al'ummar kasar suka zabi Muhamad Abdull...Farmajo a matsayin wanda zai milke su shekaru 4 masu zuwa.

A kwai babban kalu bale da ke jiran sabon Shugaban kasar Muhamad Abdull...Farmajo musaman ma matsalar fari da kuma matsalar ta'addanci na kungiyar Ashabab.

Shekaru da dama da kungiyar Ashabab ke yakar Gwamnatin Somaliya, a watan Augustan 2011 Dakarun kasar tare da hadin kan Dakarun wanzar da zaman lafiya na Kungiyar tarayyar Afirka sun fatattaki mayakan na Ashabab a manyan buranan kasar, amma har yanzu kungiyar na rike da wasu kananan kauyukan kasar.