MDD Ta Damu Kan Rikicin Tsakiyar D.R Congo
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i17553-mdd_ta_damu_kan_rikicin_tsakiyar_d.r_congo
MDD ta bayyana matukar damuwarta dangane da rikicin dake ci gaba da faruwa a tsakiyar Jamhuriya Demokuraddiyar Congo wanda kawo yanzu ya yi sanadin mutuwar gomman mutane cikin 'yan kwanaki kalilan.
(last modified 2018-08-22T06:59:40+00:00 )
Feb 11, 2017 10:47 UTC
  • MDD Ta Damu Kan Rikicin Tsakiyar D.R Congo

MDD ta bayyana matukar damuwarta dangane da rikicin dake ci gaba da faruwa a tsakiyar Jamhuriya Demokuraddiyar Congo wanda kawo yanzu ya yi sanadin mutuwar gomman mutane cikin 'yan kwanaki kalilan.

Tun a watan tara ga watan Fabrairu rikicin daya barke, wanda kuma ke ci gaba da faruwa  ke ci gaba tsakanin mayakan Kamwina Nsapu da dakarun gwamnati a yankin Tshimbulu inda mutane talatin zuwa hamsin suka rasa rasukansu.

Tawagar MDD a kasar ta DRC wato MONUSCO ta ce ta damu sosai dangane da halin da ake ciki a wannan yankin da kuma yadda mayakan na Kamwina Nsapu ke dauka yara aikin soji.

MONUSCO ta kuma damu akan yadda dakarun gwamnati ke wuce gona -da -iri a cikin aikinsu.

A sanarwar data fitar tawagar ta MONUSCO ta yi Allah wadai da ayyukan mayakan na Kamwina Nsapu, tare da kira ga dajarun gwamnatin kasar su kiyaye take hakkin bil adama su gudanar da aikinsu yadda dokoki kasar dana kasa da kasa suka tanada.