Tallafin Euro Miliyon 75 Na Tarayyar Turai Ga Kasar Gambia
(last modified Sat, 11 Feb 2017 14:58:54 GMT )
Feb 11, 2017 14:58 UTC
  • Tallafin Euro Miliyon 75 Na Tarayyar Turai Ga Kasar Gambia

Kungiyar tarayyar Turai ta bada sanarwan bada tallafin kudade Euro miliyon 75 ga gwamnatin kasar Gambai wacce ta samu sauyin shugabanci a watan da ya gabata.

Majiyar muryar jumhuriyar musulunci ta Iran ta nakalto "Neven Mimica" shugaban hukumar raya kasashen da tallafawa kasashen duniya na tarayyar Turai yana fadar haka a ranar Alhamis da ta gabata, kuma ya kara da cewa sun bada kudaden ne don tallafawa kasar Gambia ta farfado daga mummunan halin da take ciki na tattalin arzikin kasar.

Wannan taimakon dai yana zuwa ne makonni kadan daga hawan kan kujerar shugabancin kasar ta Gambiya wanda Adama Barrow yayi. Hukumar ta kara da cewa za'a kashe wadannan kudade ne a fagagen tsaro, raya tattalin arziki  da samarwa mutanen kasar ayyukan yi da kuma gina hanyoyi. 

Kafin haka dai kungiyar tarayyar ta Turai ta dakatar da tallafin da take bawa kasar ta Gambia a shekara ta 2014 bayan da tsohon shugaban Kasar Yahyaha Jame wanda ya share shekaru 22 yana shugabancin kasar da kuma wasu abubuwan da kungiyar ta EU bata ji dadi ba.

Da wannan dalili da kuma wasu da dama ne.  bayan faduwarsa a zaben ranar daya ga watan Decemba da ta gabata kasashen duniya musamman kasashen yammacin Afrika suka takurawa Yahyah Jame ya bar kujejera shugabancin kasar ya kuma shiga gudun hijira a kasar Equetorial Guinea.

Banda wannan tallafin dai, har ila yau  ana saran  sabuwar gwamnatin kasar ta Gambia za ta sami tallafin bankin duniya don farfado da tattalin arzikin kasar.

Image Caption

 

Amma masana harkokin siyada da dama suna da ra'ayin cewa taimkon da wadannan manya manyan kasashen duniya suke bayarwa ba a banzace ba. Don a mafi yawan lokuta wadan nan tallafdi sukan zo tare da wasu sharudda wanda amfaninsu zai koma ne ga wadan nan kasashe, ko kuma ya zamanto gwamnatin tana aiwatar da bukatun wadannan kasashe a kasar da suka bawa wannan tallafin, musamman a wabangaren yada al-adun da manufofin wadannan kasashen a cikin al-ummarsu.

Har'ila yau abinda ya tabbata a tarihin tallafin da manya manyan kasashen duniya kamar kasashen tarayyar turai da kuma Amurka suke bawa suke bawa kasashen duniya, wadan nan tallafi ko kadan basa taimakawa wadan nan kasashe wajen kyautata tattalin arzikin kasashen ko kuma fitar da su cikin talauci.

Banda haka wasu masanan suna ganin tallafin ta kasashen suke bawa raunanan kasashen duniya yana nufin kara yawan abokansu a kasashen duniya don mai yuwa su bukaci goyon bayansu a cikin lamura da dama musamman a majalisar dinkin duniya.

Image Caption

 

ko yaya abin ya kasance dai wadan nan tallafi dai ba na Al...da annabibane. dole ne a tattare da su akwai wasu abubuwa wanda wadan nan kasashe suke amfana da su daga kasashen da suke bawa tallafin sannan a mafi yawan lokaci tallafin ba masalahi bace ga kasashen da suke karbansu.