Nijeriya : Ana Bukatar Naira Billion 10 Don Farfado Da Kanfanin Arik Air
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i17595-nijeriya_ana_bukatar_naira_billion_10_don_farfado_da_kanfanin_arik_air
Hukuma kula da dokiyar gwamnati ta The Asset Management Corporation of Nigeria ko kuma (AMCON) ta bayyana cewa kamfanin jiragen sama na Arik Air yana bukatar Naira billion 10 don farfado da kamfanin zuwa kamar yadda take a da.
(last modified 2019-04-27T09:55:10+00:00 )
Feb 13, 2017 02:49 UTC
  • Nijeriya : Ana Bukatar Naira Billion 10 Don Farfado Da Kanfanin Arik Air

Hukuma kula da dokiyar gwamnati ta The Asset Management Corporation of Nigeria ko kuma (AMCON) ta bayyana cewa kamfanin jiragen sama na Arik Air yana bukatar Naira billion 10 don farfado da kamfanin zuwa kamar yadda take a da.

Jaridar Daily Trust ta Nigeria ta nakalto Hukumar AMCO tana cewa gwamnatin tarayyar ta karnbi iko da da harkar gudanarwa na jirginne a ranar Alhamis da ta gabata don hana rugurguzar kamfanin, wanda ake binta basussuka na kimanin naira billion 300, kuma jiragen sa guda 10 kacal suka tashi a cikin jirage 28 wanda jirgin yake da su. 

AMCO ta kara da cewa a halin yanzu kamfanin Arik Air bata da ko kudin sayan makamashin na jiragen saman da suke aiki, don babu wanda zai sayar mata da mai jirgi sai da kudi a hannu. 

Capt. Roy Ukpebo Ilegbodu, sabon shugaban kamfanin ya bayyana cewa zai yi kokarin tada jiragen kamfanin Arik Air 21 wadanda suka kasa aiki saboda dalilai daban daban nan ba da dadewa ba. Kafin haka dai kamfanin ne yake daukar kashi 55% na fasinjojin Nigeria zuwa wurare daban daban a cikin kasar da ma kasashen waje.