Yan Sandan Kenya Na Tsare Da Waji Jami'in Diplomasiyyar Amurka
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i17599-yan_sandan_kenya_na_tsare_da_waji_jami'in_diplomasiyyar_amurka
Majiyar yansanda a birnin Nairobi na kasar Kenya ta bayyana cewa suna tsare da wani jimi'in diblomasiyar kasar Amurka wanda ya aikata laifin duki a kan titunan birnin sannan ya fitar da makami ya auna direban wata motan da ya yi karo da ita.
(last modified 2019-04-27T09:55:10+00:00 )
Feb 13, 2017 02:50 UTC
  • Yan Sandan Kenya Na Tsare Da Waji Jami'in Diplomasiyyar Amurka

Majiyar yansanda a birnin Nairobi na kasar Kenya ta bayyana cewa suna tsare da wani jimi'in diblomasiyar kasar Amurka wanda ya aikata laifin duki a kan titunan birnin sannan ya fitar da makami ya auna direban wata motan da ya yi karo da ita.

Kamfanin dillancin Labaran Associated Press ya nakalto Robitson Tuku shugaban yansanda da birnin Nairobi yana fadar haka a jiya Lahadi' ya kuma kara da cewa Jami'in diblomasiyyar wanda bai ambaci sunansa ba ya jawo aukuwar wani hatsarin motu a daya daga cikin manya manyan tituna a birnin sannan ya fito da bindiga ya auna wani direban da ya jawo masa hatsari, amma bai yi harbi ba sannan daga baya ya arzce daga wurin da ya jawo hatsarin. 

Har'ila yau jami'in ofishin jakadancin Amurka a birnin Nairori ya tabbatar da wannan labarin amma ya ki yin magana kan fitar da makami da ya yi bayan hatsarin da ya jawo. 

Majiyoyi guda biyu basu bayyana cewa akwai rasa rai ko kuma raunata wani a cikin hatsarin da jami'in diblomasiyar yan jawo ba, sannan basu bayyana laifin da ake tuhumarsa da shi bayan tsare shi ba.