Ziyarar Sakataren Harkokin Wajen Kasar Birtaniya A Kasar Gambiya
(last modified Wed, 15 Feb 2017 06:22:15 GMT )
Feb 15, 2017 06:22 UTC
  • Ziyarar Sakataren Harkokin Wajen Kasar Birtaniya A Kasar Gambiya

Sakataren harkokin wajen kasar Birtaniya ya fara gudanar da ziyarar aiki a nahiyar Afrika, inda ya fara da kasar Gambiya.

A bayan isarsa kasar Gambiya a jiya Talata; sakataren harkokin wajen kasar Birtaniya Boris Johnson ya gana da sabon shugaban kasar Adama Barrow, inda suka tattauna batutuwa da dama ciki har da shirin kasar Birtaniya na taimakawa Gambiya a fagen bunkasa ilimi da farfado da harkar tattalin arzikin kasar. Tun bayan da kasar Gambiya ta samu 'yancin kai a shekara ta 1965 zuwa yanzu, babu wani daga cikin sakatarorin harkokin wajen Birtaniya da ya sanya kafarsa a cikin kasar ta Gambiya da sunan gudanar da ziyarar aiki sai Boris Johnson, don haka wannan ziyarar aikin da ya kai Gambiya ta zame mai muhimmanci gare shi.

Nasarar da Adama Barrow ya samu a zaben shugabancin kasar Gambiya a cikin watan Disamban shekarar da ta gabata ta 2016 tare da samun damar dare kan karagar shugabancin kasar bayan takaddamar da ta biyo bayan zaben da har ta kai ga tilastawa tsohon shugaban kasar Yahya Jammeh gudun hijira yana daga cikin dalilan janyo hankalin mahukuntan Birtaniya kan sake bude wani sabon shafin alaka a tsakanin kasashen biyu.

Daga cikin matakan da tsohuwar gwamnatin Gambiya karkashin shugabancin Yahya Jammeh ta dauki na raba gari da siyasar kasar Birtaniya har da matakin ficewa da kungiyar kasashen rainon Birtaniya ta Commonwealth a watan Oktoban shekara ta 2013 bayan zargin cewa; Kungiyar ta Commonwealth tana gudanar da wani sabon salon mulkin mallaka ne kan kasashen kungiyar. Kamar yadda tsohon shugaban kasar ta Gambiya Yahya Jammeh ya sanar da cire harshen Turanci da ake magana da shi a hukumance ta hanyar musanya shi da harshen cikin gida.

Tun bayan ficewar kasar Gambiya daga kungiyar rainon Birtaniya ta Commonwealth ta zame bata da alaka ta fuskar siyasa da tattalin arziki da sauran kasashen kungiyar, kamar yadda a tsawon shekaru 22 da Yahya Jammeh ya shafe yana gudanar da shugabancin kasar Gambiya an zarge shi da gudanar da mulkin kama karya tare da take hakkin bil-Adama da takaita 'yancin walwala da na siyasa a kasar.

A ganawar da ta gudana tsakanin sabon shugaban kasar Gambiya Adama Barrow da Boris Johnson sakataren harkokin wajen kasar Birtaniya a jiya Talata sun cimma matsaya kan shirin kyautata alaka tsakanin kasashensu, kamar yadda Boris Jahnson ya yi nuni da cewa nan da wasu 'yan watanni masu zuwa za a sake dawo da kasar Gambiya cikin kungiyar rainon Birtaniya ta Commonwealth, haka nan Boris Johnson ya yi furuci da cewa zabukan da aka gudanar a kasashen Gambiya da Ghana a baya bayan nan suna nuni da yadda tsarin dimokaradiyya yake ci gaba da samun habaka ne a yankin yammacin Afrika.