Gwamnatin Kasar Tunisia Zata Maida Dangantaka Da Halattanciyar Gwamnatin Kasar Siria
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i17704-gwamnatin_kasar_tunisia_zata_maida_dangantaka_da_halattanciyar_gwamnatin_kasar_siria
Ma'aikatar harkokin wajen kasar Tunisia ta bada labarin cewa gwamnatin kasar zata maida hulda da kuma aiki tare da gwamnatin kasar Siria karkashin shugabancin Shugaba Bashar Al-asad.
(last modified 2018-08-22T06:59:41+00:00 )
Feb 16, 2017 08:17 UTC
  • Gwamnatin Kasar Tunisia Zata Maida Dangantaka Da Halattanciyar Gwamnatin Kasar Siria

Ma'aikatar harkokin wajen kasar Tunisia ta bada labarin cewa gwamnatin kasar zata maida hulda da kuma aiki tare da gwamnatin kasar Siria karkashin shugabancin Shugaba Bashar Al-asad.

Kamfanin dillancin labaran Spinik n akasar Turkia ya nakalto Khamis Al-Jaheenawi ministan harkokin wajen kasar yana fadar haka. Ya kuma kara da cewa nan ba da dadewa ba gwamnatin kasar Tunisia zata aike da tawaga zuwa birnin Damascus don bincike da gano yawan yan kasar ta Tunisia wadanda suka yakar gwamnatin kasar ta Siria tare da yan ta'adda.

Tawagar har'ila yau imji Ministan zata karbi yan ta'adda yan asalin kasar ta Tunisia wadanda suke tsare a gidajen yari na kasar ta Siria. 

Ministan harkokin wajen kasar ta Tunisia ya bayyana cewa gwamnatin kasar Jamus ma ta shaida mata kan cewa zata dawo da yan aslin kasar 1500 wadanda suka shiga kasar ba bisa ka'ida ba..

Daga karshe ministan ya bayyana cewa bayan an dawo da su gida, za'a gurfanar da su a gaban kotu don yanke masu hukuncin da ya dace da laifuffukansu.