Gwamnatin Nigeria Ta Amince Da Wani Sabon Tsarin Kiwon Lafiya A Kasar
Gwamnatin tarayyar Nigeria ta amince da wani sabon tsarin kiwan lafiya a kasar.
Jaridar Premiumtimes ta nakalto ministan lafiya Isaac Adewole, yana fadar haka a jiya Laraba bayan kammala taron majalisar ministoci na mako mako a fadar shugaban kasa.
Isaac Adewole, ya kara da cewa sabon tsarin kiwon lafiya a kasar, shi ne na ukku a tarihin kasar bayan tsari na 1988 da kuma ta 2004. Kuma wannan tsarin zai bada fifiko wajen tabbatar da cibiyoyin kiwon lafiya a kasar da kuma asbitoci suna aiki yanda yakamata. Sannan sabon tsarin zai maida kiwon lafiya a mataki na farko ya zama shine gintsikin kiwon lafiya a kasar.
Banda haka miunistan ya kammala da cewa sabon tsarin zai hada da tallafawa dukkan bangaririn kiwon lafiya da zasu kawo ci gaba a lafiyan mutanen kasar kai tsaye.