Ministan Kwadago Na Sudan Ta Kudu Ya Yi Murabus
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i17738-ministan_kwadago_na_sudan_ta_kudu_ya_yi_murabus
Ministan kwadago na Sudan ta kudu ya sanar da yin murabus dinsa daga bakin aiki tare da kuma mika kai ga jagoran 'yan adawa na kasar.
(last modified 2019-08-10T14:54:46+00:00 )
Feb 17, 2017 16:43 UTC
  • Ministan Kwadago Na Sudan Ta Kudu Ya Yi Murabus

Ministan kwadago na Sudan ta kudu ya sanar da yin murabus dinsa daga bakin aiki tare da kuma mika kai ga jagoran 'yan adawa na kasar.

A cikin sanarwar murabus dinsa, Mista Gabriel Duop Lam, ya ce ''daga wannan ranar ta 17 ga wata Fabrairu 2017 na yi murabus daga mukami na ministan kwadigo kana na mika kai ga jam'iyyar adawa ta SPLM?SPLA-IO ta Riek Machar.

Gwamnatinm kasar ta Sudan ta kudu a ta bakin ministan yada labarenta, Michael Makuei, ta tabbatar da hakan, tare da cewa murabus din ba shi da wata illa a gare ta, kuma hakan da yayi daidai ne domin yana da 'yancin yin hakan.

A watan Afrilu na shekara 2016 ne aka nada Mista Duop ministan Kwadago a cikin gwamnati a lokacin da madugun 'yan adawa na kasar kana jagoran 'yan tawaye ya koma Juba domin kama aiki a matsayinsa na mataimakin shugaban kasar Salva Kiir kamar yadda yarjejeniyar watan Agusta 2015 ta tanada, saidai sabanin baraka data kunno kai tsakanin dakarun bangarorin biyu, Mista Mashar ya sake ficewa daga Juba inda yanzu haka yake gudun hijira a Afrika ta Kudu.

Murabus din Mista Diop dai na zuwa kwanaki kadan bayan murabus din da Janar Thomas Cirillo Swaka na rundinar sojin kasar ya yi domin kalubantar yadda dakarun gwamnatin kasar suka ki mutunta yarjejeniyar zamen lafiya da aka cimma a watan Agusta na 2015 da kuma yakin kabilancin da sukeyi.