Nijeriya : Kotun Daukaka Kara Ta Ce Ali Modu Sherif Ne Shugaban PDP
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i17742-nijeriya_kotun_daukaka_kara_ta_ce_ali_modu_sherif_ne_shugaban_pdp
Kotun daukaka kara dake birnin Fatakwal a Jihar Ribas da ke kudancin Najeriya ta tabbatar da Ali Modu Sheriff a matsayin cikakken shugaban Jam’iyyar PDP mai adawa a kasar.
(last modified 2018-08-22T06:59:41+00:00 )
Feb 17, 2017 13:54 UTC
  • Nijeriya : Kotun Daukaka Kara Ta Ce Ali Modu Sherif Ne Shugaban PDP

Kotun daukaka kara dake birnin Fatakwal a Jihar Ribas da ke kudancin Najeriya ta tabbatar da Ali Modu Sheriff a matsayin cikakken shugaban Jam’iyyar PDP mai adawa a kasar.

Wannan hukuncin da kotun ta yanke a yau Juma'a ya soke waccen hukuncin da kotun tarayyar da ke jihar ta Ribas ta zartas da ke bayyana Sanata Ahmed Makarfi a matsayin shugaban Jam’iyyar. 

A watan Mayu na shekara data gabata ne jam’iyyar PDP ta kore Shugabanta na kasa Ali Modu Sheriff, tare da nada tsohon gwamnan Kaduna Ahmed Makarfi a matsayin shugaban rikwan kwarya.

Kuma a waccen lokacin jam’iyyar ta ce ta dau matakin ne domin shawon kan rigingimun da suka mamaye ta.

Babbar jam’iyyar adawa ta kasar dai ta tsunduma cikin rikicin shugabanci tun bayan da ta sha kayi a zaben shekara 2015.