Sudan Ta Kudu: Wani Babban Jami'in GWamnati Ya yi Murabus.
Alkalin kotun soja na kasar Sudan ta kudu Khalid Uno Loky ya yi murabus daga mukaminsa saboda kin amincewa da yaduwar cin hanci da rashawa da kuma kalibanci.
Alkalin kotun soja na kasar Sudan ta kudu Khalid Uno Loky ya yi murabus daga mukaminsa saboda kin amincewa da yaduwar cin hanci da rashawa da kuma kalibanci.
Kamfanin dillancin labarun Associated Press wanda ya nakalto labarin ya ci gaba da cewa; A cikin mako guda, Khalid Uno Loky shi babban jami'in gwamnati na uku wanda ya yi murabus, saboda kin amincewa da salon mulkin Silva Kiir.
A cikin bayanin da ya fitar a jiya juma'a Khalid Uno Loky ya ce; Tsarin kotunan kasar, ya ginu ne bisa cin hanci da rashawa da kuma kabilanci.
Kungiyoyin kare hakkin bil'adama na kasar Sudan ta kudu da dama sun soki sojojin kasar saboda abinda su ka kira aikata laifukan yaki da su ke tafkawa.