Yadda Manyan Sojoji Ke Juyawa Gwamnatin Salva Kiir Baya
-
Ana zargin shugaba Kiir dan kabilar Dinka, da ba da izinin kashe duk wani da ba kabilarsa ba.
A Sudan ta Kudu ana ci gaba da samun manyan jami'an soji dake juyawa gwamnatin kasar baya ta hanyar yin murabus daga bakin aikinsu.
Sojojin dai na zargin shugaba Salva Kiir da hannu a yakin basasa da kabilancin da kasar ta samu kan ta a ciki yau da shekaru uku.
Murabus din baya bayan nan wanda kuma shi ne na uku a cikin mako guda, shi ne na Janar Henry Oyay Nyago, wanda ya zargi shugaba Kiir wanda ya fito daga kabilar Dinka, da ba da izinin kashe duk wani farar hula da ba kabilarsa ba.
Janar Nyago, wanda launa ne kana babban darecta janar na kotun sojin shi ne mutum na uku wanda ya mika takardar murabus dinsa ga shugaba Salva Kiir wanda ya zarga da aikata laifukan yaki.
A cikin takardar murabus dinsa Janar Nyago ya ce ban zan iya rufe ido ba akan irin kisan kiyashi da laifukan yaki da ake ci gaba da aikatawa bisa umurnin shugaba Salva Kiir.
Shi kuwa a nasa bangare Kanal Khalid Ono Loki, ya zargi shugaban hafsan sojin kasar da kamewa da garkame wadanda ba 'yan kabilar shugaban kasar ba.
A cikin takardar murabus din daya mikawa babban hafsan sojin kasar Paul Malong Awan, wace kanfanin dilancin labaren AFP ya samu irinta, Kanal Loki, ya soki yadda ake kame wadanda ba 'yan kabilar shugaban kasar ba, tare da garkame su ba tare da wata kwarara hujja ba ko kuma takamaiman laifin da ake zarginsu da shi ba, kuma su kwashe lokaci mai tsawo ba tare da anyi musu shari'a ba.
Ko a makon da ya gabata Laftana Kanal Thomas Cirillo Swaka, ya mika tashi takardar yin murabus din, bayan zargin shugaba Salva Kiir da abin daya kira kokarin share duk kabilar da ta bata shi ba a Sudan ta Kudun.
Koda yake kawo yanzu, babu wani martani da sojojin kasar ko gwamnati suka maida kan wadannan zarge-zargen, aman tuni wasu suka fara sokaci akan yadda hakan ya fara fiddo a fili zargin kisan kiyashin fararen hula da aka dade anayiwa Shugaba Salva Kirr a wannan kasar ta sudan ta Kudu.
Ko baya ga mayan sojojin da sukayi murabus da akwai ministan Kwadigo na kasar Sudan ta Kudu, Gabriel Duop Lam, da ya yayi murabus tare da mika wuya ga jagoran 'yan adawa na kasar Riek Mashar.
A watan Afrilu na shekara 2016 ne aka nada Mista Duop ministan Kwadago a cikin gwamnati a lokacin da madugun 'yan adawa na kasar kana jagoran 'yan tawaye ya koma Juba domin kama aiki a matsayinsa na mataimakin shugaban kasar Salva Kiir kamar yadda yarjejeniyar watan Agusta 2015 ta tanada, saidai sabanin baraka data kunno kai tsakanin dakarun bangarorin biyu, Mista Mashar ya sake ficewa daga Juba.
Rikicin Sudan ta Kudu daya barke a shekara 2013 ya yi sanadin mutuwar dubun dubatar mutane tare da cilastawa sama da Miliyan uku kauracewa muhallansu.