An Tabbatar Da Mutuwar 18 A Harin Ta'addancin Birnin Mogadishun Somaliya
(last modified Mon, 20 Feb 2017 06:23:46 GMT )
Feb 20, 2017 06:23 UTC
  • An Tabbatar Da Mutuwar 18 A Harin Ta'addancin Birnin Mogadishun Somaliya

Rahotanni daga kasar Somaliya sun tabbatar da cewa adadin mutanen da suka mutu a wani harin ta'addanci da aka kai birnin Mogadishu, babban birnin kasar a jiya Lahadi sun kai mutane 18 kan wasu sama da 25 kuma sun sami raunuka.

Rahotannin sun bayyana cewar harin dai an kai shi ne da wata mota da aka shake ta da bama-bamai inda 'yan ta'addan suka  tarwatsa ta yankin da ke makare da jama'a a safiyar Jiya Lahadi.

Wannan harin dai shi ne hari na farko da aka kai birnin Mogadishun  tun bayan  zaben shugaban kasar da aka gudanar inda aka zabi sabon shugaban kasar, Mohammed Abdullahi Mohammed.

Ana jingina irin wadannan hare-haren dai ga 'yan kungiyar ta'addancin nan ta Al-Shabab musamman ma dai yadda kwamandan kungiyar ya sha alwashin kai hari ga duk wanda ya bai wa sabon shugaban kasar hadin kai.