MDD tayi alawadai kan harin ta'addancin da aka kai Somaliya
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i17844-mdd_tayi_alawadai_kan_harin_ta'addancin_da_aka_kai_somaliya
Manzon musaman na MDD a Kasar Somaliya yayi alawadai kan harin ta'addancin da aka kai wata kasuwa a birnin Magadushu fadar milkin kasar Somaliya.
(last modified 2018-08-22T06:59:42+00:00 )
Feb 20, 2017 08:31 UTC
  • MDD tayi alawadai kan harin ta'addancin da aka kai Somaliya

Manzon musaman na MDD a Kasar Somaliya yayi alawadai kan harin ta'addancin da aka kai wata kasuwa a birnin Magadushu fadar milkin kasar Somaliya.

Kamfanin dillancin labaran Xin Huwa na kasar China ya nakalto Michael Keating manzon musaman na MDD kan kasar Somaliya na yin alawadai kan mumunan harin ta'addancin da aka kai birnin Magadushu tare da bayyana cewa kisan fararen hula ta'addanci ne kuma wajibi ne a gaggauta zagulo wadanda suka aikata wannan aika-aika domin meka su gaban Kotu.

Rahotonni sun bayyana cewa: Wani dan kunan bakin wake da ya makare motarsa da bama-bamai ya kusa cikin wata kasuwa a birnin Mogadishu fadar mulkin kasar Somaliya a jiya Lahadi, inda ya tarwatsa kansa a tsakanin jama'a lamarin da ya janyo hasarar rayukan mutane akalla 20 tare da jikkata wasu fiye da 30 na daban.

A yayin da ziyarci wadanda suka jikkata asibiti a wannan Litinin, Shugaban kasar Muhamad Abdul...Farmaju ya ce zai bayar da kautar dala dubu 100 ga wanda ya taimaka aka kamo wadanda suka kai wannan mumunan hari na ta'addanci.