Guinea : An Kashe Mutane Biyar A Cikin Masu Zanga-zanga
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i17862-guinea_an_kashe_mutane_biyar_a_cikin_masu_zanga_zanga
Rahotannin daga Guinea na cewa a kalla mutane biyar ne suka mutu a yayin zanga-zangar neman sake bude azuzuwa a Conakry babban birnin kasar.
(last modified 2019-04-27T09:55:10+00:00 )
Feb 21, 2017 02:24 UTC
  • Guinea : An Kashe Mutane Biyar A Cikin Masu Zanga-zanga

Rahotannin daga Guinea na cewa a kalla mutane biyar ne suka mutu a yayin zanga-zangar neman sake bude azuzuwa a Conakry babban birnin kasar.

Wata majiyar asibiti Igance Deen dake birnin na Conakry ta shaidawa kanfanin dilancin labaren AFP cewa mutanen da suka hada da maza hudu da kuma mace guda sun mutu ne sanadin raunukan da suka samu ta hanyar harbi da harsashin bindiga da aka musu.

Masu zanga zangar dai na bukatar da a sake bude makarantun da gwamnati ta rufe saboda yajin aikin maluman makarantu.

Bisa alkalumen da gwamnati ta fitar ta ce mutane 30 ne suka raunana a yayin zanga zangar ciki har da jami'an tsrao.

A makonnin da suka gabata dai malumen makarantu kasar suka shiga yaje yaje aiki, lamarin daya cilastawa gwamnati rufe makarantun.