Bukatar taimako na Gwamnatin Kenya domin kalubalantar Fari a kasar
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i17892-bukatar_taimako_na_gwamnatin_kenya_domin_kalubalantar_fari_a_kasar
Gwamnatin kasar Kenya ta bukaci taimakon kungiyoyin kasa da kasa domin kalubalantar matsalar fari da kasar ke fuskanta.
(last modified 2018-08-22T06:59:43+00:00 )
Feb 21, 2017 08:17 UTC
  • Bukatar taimako na Gwamnatin Kenya domin kalubalantar Fari a kasar

Gwamnatin kasar Kenya ta bukaci taimakon kungiyoyin kasa da kasa domin kalubalantar matsalar fari da kasar ke fuskanta.

َGwamnatin kasar Kenya ta shelanta neman taimokon kungiyoyin kasa da kasa na tsabar kudi kimanin  miliyan 114 na Dalar Amurka domin kalubalantar matsakar karamcin abinci da kasar ke fuskanta. 

Cikin wata sanarwa da ta fitar a wannan Talata, Gwamnatin ta Kenya ta ce saboda matsalar fari, wasu daga cikin 'yan kasar na fuskantar karamcin abinci,kuma daga cikin mutane miliyan daya dubu dari uku da suke fuskantar matsalar karamcin abinci daga watan Augustan da ya gabata, adadin ya karu zuwa miliyan uku a wannan wata na favrayu da muke ciki, baya ga wannan matsala, farashin kayan abinci ya karu da kashi 20%.

Kakakin Gwamnatin ta Kenya ya kara da cewa ya zuwa yanzu Gwamnati ta ware miliyan 73 domin kalubalantar wannan matsala ta karamcin abinci a kasar kuma a matakin farko an kashe dala miliyan 45.