An Sake Kafa Dokar Hana Fita Ta Sa'o'ee 24 A Kudancin Kaduna
Majalisar tsaro ta Jihar Kaduna a tarayyar Nigeria ta kafa dokar hana fita na sa'o'i 24 a wasu yankuna a kudanci Kaduna don shawo kan karin kashe kashen da ke aukuwa a yankin.
A wata sanarwan wacce Samuel Aruwa mai bawa gwamna shawara ta musmman kan harkokin watsa labarai ya sanya wa hanyu a yau Talata, ya ce hakan ya zama dole don kare rayuka da dukiyoyi a wadan nan yankuna.
Sanarwan ta kara da cewa yankunan da dokar ta shafa sun hada da kananan hukumomi na Jama'a da kuma Kaura, inda aka sami wasu yan bindiga da suka kutsa cikin yankin suka kashe mutane da dama a cikin makon da muke ciki.
har'ila yau majalisar tsaron ta bukaci dukkan jami'an tsaron da suke kula da wadan nan yankuna su tabbatar da cewa an bi umurnin hana fitan, sai wadanda suke da ayyukan lalura wadanda suka hada da jami'an bada agaji ko na asbitoci, su dimma tare bada cikekken hadin kai ga jami'an tsaron.
A jiya Litinin ne aka bada labarin cewa wani dan bindiga ya shiga kauyen Ashin na karamar hukumar kaura ya kashe mutane akalla 14 sannan ya raunata wasu da dama. banda haka a ranar lahadi ma an kai irin wannan harin a bakin kogi, da kauyen Kaninko a karamat hukumar Jama'a .