Rundunar Sojin Najeriya Ta Yi Watsi Da Rahoton Amnesty
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i17938-rundunar_sojin_najeriya_ta_yi_watsi_da_rahoton_amnesty
Rundinar sojin Najeriya ta yi fatali da rahoton da kungiyar kare hakkin bil adama ta Amnesty International ta fitar, wanda ya zarge ta da toye hakkin bil adama da kuma kisan fararen hula a yakin da take da kungiyar Boko Haram.
(last modified 2018-08-22T06:59:43+00:00 )
Feb 23, 2017 02:12 UTC
  • Rundunar Sojin Najeriya Ta Yi Watsi Da Rahoton Amnesty

Rundinar sojin Najeriya ta yi fatali da rahoton da kungiyar kare hakkin bil adama ta Amnesty International ta fitar, wanda ya zarge ta da toye hakkin bil adama da kuma kisan fararen hula a yakin da take da kungiyar Boko Haram.

Kakakin rundunar sojin Najeriya Birgediya Janar Rabe Abubakar, ya karyata rahoton na Amnesty wanda ya danganta da marar tushe balle ma'ana. 

Rahoton na baya bayan nan da Amnesty ta fitar ya zargi dakarun sojin kasar da hallaka fararen hula 240, ciki hadda jarirai a jihar Borno, da kuma wasu mutanen su 177 dake goyon bayan kafuwar kasar Biafra.

Da yake mai da martani game da rahoton a birnin Abuja, fadar mulkin kasar, Rabe Abubakar, ya ce  yana fatan al'umma za su yi watsi da daukacin rahoton, duba da cewa, a baya ma kungiyar ta Amnesty, ta sha fidda makamancin wannan rahoto, inda take zargin sojoji da sauran jami'an tsaron kasar da aikata laifuka, ba tare da wata gamsasshiyar hujja ba.

Kaza lika Rabe ya zargi Amnesty International da kitsa bayanai na kashin kai, domin cimma wata manufofin ta na daban, tare da yunkurin jefa shakku a zukatan 'yan Najeriya, game da irin ayyukan da sojojin kasar ke yi na kakkabe bata gari daga sassan arewa maso gabashin kasar.