Guinea : An Sake Bude Makarantu Bayan Yajin Aikin Makwanni 3
Rahotanni daga Guinea na cewa an sake bude makarantun boko a Guinea bayan kasancewarsu a rufe na tsawan makwanni uku saboda yajin aiki na malumen makarantu.
Hakan dai ya biyo bayan yarjejeniyar da kungiyoyin malumane makarantun suka cimma da gwamnatin kasar a ranar Litini data gabata.
A ranar 1 ga watan Fabaruru na wannan shekara ne gwamnatin kasar ta dau matakin rufe makarantun saboda yajin aikin malumen da kuma zanga-zanga data ki karewa.
Yajin aiki dai ya hada kungiyoyin malumen makarantun dake neman karin albashi da kuma masu neman ayi masu daukar aiki ta din-dindin.
Alkalumen da mahukutan kasar suka fitar sun nuna cewa mutane biyar ne suka mutu kana wasu da dama ciki har da jami'an tsaro suka raunana a mumunar zanga zangar baya bayan nan a Conakry babban birnin kasar.