An karfafa matakan tsaro a jihar Kaduna
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i17974-an_karfafa_matakan_tsaro_a_jihar_kaduna
Bayan barkewar rikcin kabikanci a wani yanki na Jihar Kaduna, Gwamnati ta sanya dokar ta bace na tsahon sa'o'i 24
(last modified 2018-08-22T06:59:43+00:00 )
Feb 24, 2017 01:26 UTC
  • An karfafa matakan tsaro a jihar Kaduna

Bayan barkewar rikcin kabikanci a wani yanki na Jihar Kaduna, Gwamnati ta sanya dokar ta bace na tsahon sa'o'i 24

Cikin wata sanarwa da ya fitar a daren jiya Alkhamis,Kakakin Gwamnan Jihar Kaduna Samuel Aruwan ya bayyana cewa sakamakon rikicin da ya barke a wasu yankunan Jihar, an samu asarar rayukan Mutane akalla 14 domin dawo da kwanciyar hankali Gwamnati ta dauki matakin sanya dokar ta bace na sa'o'i 24 a yankunan domin baiwa Jami'an tsaro damar gudanar da aiyukansu.

Rahotanni sun bayyana cewa rikicin ya faru ne tsakanin Makiyaya da Manona a kan wurin kiyo da ban ruwan busashe, lamarin da ya kara  matsin lamba ga magabatan jihar.

Shugaban 'yan sandar jihar kaduna Aghole Abeh ya sanar a jiya Alkhamis cewa sun tura Jami'an 'yan sanda na musaman a yankunan da rikicin ya auku, domin gawo karshen rikcin da kuma hana shi yaduwa zuwa sauren yankunan Jihar.

Bisa rahoton da Ma'aikatar dake kula da tashe-tashen hankula a Jihar ta Kaduna ta fitar , daga farkon wannan shekara ta 2017 zuwa yanzu kimanin Mutane 200 ne suka rasa rayukansu sanadiyar barkewar rikici a kudancin jihar ta Kaduna.