Najeriya: Neman Kudin Fansar Sakin Jamusawan Da Ake Garkuwa Da Su.
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i17990-najeriya_neman_kudin_fansar_sakin_jamusawan_da_ake_garkuwa_da_su.
Kamfanin Dillancin Labarun Associated Press ya ambato cewa; Wadanda su ka yi garkuwa da jamusawa biyu a Najeriya, suna bukaci a basu dala dubu dari biyu ( 200,000) kafin sakinsu.
(last modified 2018-08-22T06:59:44+00:00 )
Feb 24, 2017 15:39 UTC
  • Najeriya: Neman Kudin Fansar Sakin Jamusawan Da Ake Garkuwa Da Su.

Kamfanin Dillancin Labarun Associated Press ya ambato cewa; Wadanda su ka yi garkuwa da jamusawa biyu a Najeriya, suna bukaci a basu dala dubu dari biyu ( 200,000) kafin sakinsu.

 farfesa Peter Bronig masanin tarihi da kuma mai taimaka masa, Yohanus Behrigar an sace su ne a jahar kaduna da ke arewacin Najeriya.

Jami'an tsaron Najeriya sun baza komarsu a neman wadanda su ka yi garkuwa da mutanen a cikin dajukan da su ke zageye da kaduna.

Malamin tarihin dai ya ce kaduna domin gudanar da nazabi da bincike akan dadaddiyar al'adar mutane Nok da ke kaduna, da ake dauka a matsayin mafi dadewar mutanen da zuwa yanzu aka gano sun rayu a Najeriya.

Sace mutane ya zama ruwan dare a Najeriya domin karbar fansa.