Zimbabuwe : Akwai Lokacin Da Mutum Ba Zai Ga Badi Ba, Inji Mugabe
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i18016-zimbabuwe_akwai_lokacin_da_mutum_ba_zai_ga_badi_ba_inji_mugabe
Shugaban Robert Mugabe na Zimbabuwe wanda ya yi bikin cika shekarunsa 93 da haihuwa a cikin wannan mako ya tabo batun mutuwarsa, tare da nisanta duk wani batu na ya janye daga mulki. 
(last modified 2018-08-22T06:59:44+00:00 )
Feb 25, 2017 12:48 UTC
  • Mugabe ya yi bikin cika shekaru 93 a duniya
    Mugabe ya yi bikin cika shekaru 93 a duniya

Shugaban Robert Mugabe na Zimbabuwe wanda ya yi bikin cika shekarunsa 93 da haihuwa a cikin wannan mako ya tabo batun mutuwarsa, tare da nisanta duk wani batu na ya janye daga mulki. 

Mugabe ya fada a jawabin nasa cewa ''dole ne akwai lokacin da ko mutun na so ba zai ga badi ba'' inda ya kara da cewa wanna muke kira ubangiji shi ne kawai ya iya yanke cewa ko zaka ci gaba da rayuwa ko kuma A'a.

Duk da yanayin rashin karfin jikinsa da kuma tabarbarewar tattalin arzikin kasarsa Mugabe na kwadayin syin tazarce a zaben shugabancin kasar na 2018.

Robert Mugabe dai ya shiga shekarunsa 37 akan karagar mulki, wanda ya sanya shi ne wani shugaban kasa mafi dadewa kan madafun iko a doron duniya nan.

Jamiyyarsa dake mulkin kasar ta ZANU-PF ce ta shirya gagarumin bikin wanda dubban jama'ar kasar suka halarta a birnin Bulawayo.

Tun shekara ta 1980 ne Shugaba Robert Mugabe ke rike da madafun iko, a kasar Zimbabuwe, kuma an kwashe mako daya ke nan ana ta bukin cika shekarun na sa 93, inda wasu bayanan ke cewa an kashe kudaden da suka haura $ Amurka miliyan daya wajen bukin.