Rikicin Neman Mulki Na Kara Bayyana Cikin Kungiyar Boko Haram
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i18036-rikicin_neman_mulki_na_kara_bayyana_cikin_kungiyar_boko_haram
A wani abu da ake ganinsa a matsayin ci gaba da sabani da rikicin neman mulki da ke faruwa tsakanin jami'ai da kwamandojin kungiyar Boko Haram ta Nijeriya, shugaban kungiyar Abubakar Shekau ya sanar da kashe kakakin kungiyar Abu Zinnira saboda kokarin kashe shi da yayi.
(last modified 2018-08-22T06:59:44+00:00 )
Feb 26, 2017 02:23 UTC
  • Rikicin Neman Mulki Na Kara Bayyana Cikin Kungiyar Boko Haram

A wani abu da ake ganinsa a matsayin ci gaba da sabani da rikicin neman mulki da ke faruwa tsakanin jami'ai da kwamandojin kungiyar Boko Haram ta Nijeriya, shugaban kungiyar Abubakar Shekau ya sanar da kashe kakakin kungiyar Abu Zinnira saboda kokarin kashe shi da yayi.

Shugaban kungiyar Boko Haram din, Abubakar Shekau, ya sanar da hakan ne cikin wani faifan sauti da wasu kafafen watsa labarai suka samu wanda kuma daga dukkan alamu taro ne na manyan jami'ai da kwamandojin kungiyar inda a ciki yake tabbatar da cewa shi ne ya kashe Abu Zinnira wanda aka fi sani da 'Tasiu'. 

Shi dai Abu Zinnira ya sha fitowa a wasu sanarwar kungiyar a matsayin kakakinta. Rahotannin dai sun bayyana cewar Shekau din ya kashe shi ne bayan zarginsa da yayi da kokarin yi masa juyin mulki da kuma kashe shi.

Bayyanar wannan faifan sautin dai yana nuni ne da irin gagarumin sabani da rikicin da ke tsakanin 'yan kungiyar  ta Boko Haram wacce ya zuwa yanzu ta yi sanadiyyar mutuwar alal akalla mutanen dubu 20 a jihohin arewa maso gabashin Nijeriya din.