An kubutar da Jamusawan da aka Garkuwa da Su a Jihar Kaduna
Jami'an tsaro a Najeriya sun yi nasarar kubutar da wasu jamusawa biyu kwararru a ilimin kimiyar gano halittu da suka dade da mutuwa a cikin kasa da aka yi garkuwa da su a Arewacin Najeriya.
A wani jawabi da ya gabatar a wannan Lahadi Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufa'i ya yaba wa jami'an tsaro kan yadda suka yi nasara wajen kubutar da wadannan Jamusawa. Sai dai babu karin bayani ko an kama wadanda suka yi garkuwar da sun.
Rahotanni sun ce Tun farko 'yan bindiga sun nemi a biyasu kudin fansa na Naira miliyan 60 kimanin (Dala $200,000) kafin su saki jamusawan
A ranar Larabar da ta gabata ce wasu Mutane dauke da makamai da ake kautata zaton masu garkuwa da Mutane ne domin neman kudin fansa suka yi awan gaba da jamusawan biyu a kauyen Jenjela da ke Jihar Kaduna. a yayin sace Jamusawan, 'yan bindigaar sun kashe wasu mazauna kauyen biyun a yayin da suka yi kokarin kubutar da su. bayan wannan hari, Jami'an tsaron Najeriya sun bayyana cewa Jamusawan sun yi kuskuran tafiya kauyen ba tare da masu kare lafiyar su ba. a halin da ake ciki tuni Jami'an tsaron Najeriya suka meka Jamusawan ga Ofishin Jakadancin kasar su dake birnin Abuja.