Yunkurin kara wa'adin Shugaban kasa a Masar
'Yan Majalisar Dokokin Masar sun bukaci kara wa'adin shugabancin kasar
Kamfanin dillancin labaran Pars na kasar Iran ya nakalto Isma'il Nasrudin wani Dan Majalisar dokoki na kasar Masar na cewa yan Majalisa na kokari wajen ganin an kara wa'adin shugabancin kasa daga shekaru 4 zuwa shekaru 6, domin a halin da ake cikin shekaru 4 ba za su isa Shugaban kasar ya gudanar da shirin ba gami da nauyin da Al'umma ta dora masa.
Dan Majalisar ya kara da ce a halin da ake ciki Majalisar na fara tattara sanya hanun 'yan kasar da nufin canza tsarin milkin kasar wanda zai karawa shugaban kasar karfin milkin da yake da shi a kundin tsarin milkin kasar.
Majalisar Dokokin ta Masar dai ta kafu ne bayan da Shugaba Abdul-fatah Alsese ya dare kan karagar milki, inda jam'iyun 'yan adawa suka kauracewa zaben, wanda hakan ya sanya wasu 'yan kasar ke ganin ta a matsayin Majalisar jeka na fika.
A shekarar 2013 ne Shugaba Alsese ya yi wa zababbiyar Gwamnatin Muhamad Mursi juyin milki bayan rikicin da yaki ci ya ki cinyewa tsakanin sa da kungiyoyin matasan kasar.