Morocco Za Ta Janye Daga Yankin Saharawi
Kasar Marocco ta ce za ta janye daga yankin Saharawi wanda aka jima ana takkadama akansa wanda kuma ya haifar da zamen tankiya tare da 'yan a ware na ''Polisario''.
Wata sanarwa da ma'aikatar harkokin wajen masarautar Maroccon ta fitar ta ce, ta ce kasar bisa rajin kan ta za ta janye daga yankin mai suna ''Guerguerat'' dake kusa da iyaka da kasar Mauritaniya a kudu maso yamma na yankin yammacin Sahara.
Matakin janyewar Marocco daga yankin bisa umurnin sarkin kasar Muhammad na shida, ya biyo bayan tattaunawar da babban sakatare na MDD, Antonio Guterres, ya yi da sarkin na Marocco a ranar Juma'a data gabata.
Sanarwar da Marocco ta fitar ta ce tana fatan bukatar da babban sakatare na MDD ya mika mata kuma tayi na'am da ita zata taimaka wajen kawo saukin shige da fice da kuma mutunta yarjejeniyar tsagaita wuta a yankin.
Yankin hamada na Saharawi wanda turawan Spain sukayi wa mulkin mallaka ya kasance karkashin ikon Marocco tun 1975, kuma tun lokacin ne 'yan Polisario ke neman pallewa daga kasar Maroccon.