Gambiya: Shugaban Kasa ya Sauke Babban Hafsan Hafsoshin Sojojin Kasar Daga Mukaminsa.
(last modified Tue, 28 Feb 2017 08:07:17 GMT )
Feb 28, 2017 08:07 UTC
  • Gambiya: Shugaban Kasa ya Sauke Babban Hafsan Hafsoshin Sojojin Kasar Daga Mukaminsa.

Majiyar Sojan Kasar ta Gambiya ta ce; Shugaban Kasar, Adama Barrow, ya sauke Usman Baji daga kan mukaminsa na hafsan hafsoshin sojojin kasar.

Majiyar ta ci gaba da cewa shugaban kasar ya kuma nada Massaneh Kinteh a matsayin sabon hafsan hafsoshin kasar.

Usman Baji ya rike mukamin hafsan hafsohin sojan kasar ta Gambiya ne tun a 2012. A lokacin takaddamar zaben kasar ya goyi bayan shugaba Yahya Jammeh, sai dai daga baya ya sauya matsayinsa yayin da kungiyar tattalin arziki ta yammacin Afrika ta yanke amfani da karfin soja.

Shekaru 22 Yahyah Jammeh ya yi akan karagar mulkin kasar ta Gambiya. Matsin lambar kasashen yankin yammacin nahiyar Afirka ta tilasta masa yin murabus daga kan mukamin nashi.