Damuwa Majalisar Dinkin Duniya Akan Yiyuwar Bullar Fari A Gabacin Nahiyar Afirka.
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i18090-damuwa_majalisar_dinkin_duniya_akan_yiyuwar_bullar_fari_a_gabacin_nahiyar_afirka.
Bayanin da majalisar dinkin duniya ta fitar akan yiyuwar bullar fari, ya ce zai jefa mutane miliyan 20 da su ke fama da rashin abinci mai gin ajiki, cikin mawuyacin hali.
(last modified 2018-08-22T06:59:45+00:00 )
Feb 28, 2017 04:37 UTC
  • Damuwa  Majalisar Dinkin Duniya Akan Yiyuwar Bullar Fari A Gabacin Nahiyar Afirka.

Bayanin da majalisar dinkin duniya ta fitar akan yiyuwar bullar fari, ya ce zai jefa mutane miliyan 20 da su ke fama da rashin abinci mai gin ajiki, cikin mawuyacin hali.

Kafar watsa labaru ta Africa Times ta ce; Majalisar Dinkin Duniyar ta bayyana yake-yaken da ake yi a cikin wasu kasashen yankin a matsayin musabbabin fadawar yankin cikin rashin abinci wanda zai zama wata babbar matsala.

Bayanin wanda Majalisar Dinkin Duniya ta fitar a ranar a jiya litinin ya kuma ce; Kasashen da za su fuskanci matsalar sun kunshi Somaliya da Djibouti da Kenya da Uganda da Sudan ta kudu.

Sai dai kasashen Sudan ta Kudu da kuma Somaliya ne za su fi fuskantar rashin abincin. A cikin Sudan ta kudu da akwai mutane miliyan hudu da dubu dari tara, sai kuma mutane miliyan biyu da dubu dari tara da su ke fama da karancin abinci mai gina jiki.