Gwamnatin Somaliya Ta Sanar Da Cewa: Kasar Tana Fuskantar Mummunar Matsalar Fari
Sabon shugaban kasar Somaliya ya bayyana cewa: Kasarsa tana fuskantar mummunar matsalar fari, don haka ya jaddada yin kira ga kungiyoyin kasa da kasa da su hanzarta kawo dauki.
A bayanin da ya fitar a jiya Talata: Shugaban kasar Somaliya Muhammad Abdullahi Muhammad Farmajo ya bayyana tsananin damuwarsa kan yadda matsalar fari tayi mummunar tasiri kan al'ummar Somaliya a shekarar da ta gabata; Sakamakon haka ya jaddada yin kira ga kungiyoyin kasa da kasa kan hanzarta daukan matakin kawo dauki domin 'yantar da al'ummar Somaliya daga mummunar barazanar fari da take tunkararsu a wannan shekara.
Hukumar kula da abinci ta Majalisar Dinkin Duniya a ranar Litinin da ta gabata ma ta fitar da bayanin gargadi kan yadda masifar fari ke barazana ga al'ummar Somaliya sakamakon rashin kyau amfanin gona a daminar data gabata lamarin da zai wurga rayuwar mutane kimanin miliyan 1.5 cikin mawuyacin halin rayuwa.