DRC : Jami'an Tsaro Sun Aikata Ba Daidai Ba, Inji MDD
Majalisar dinkin duniya ta fitar da wani rahoto wanda a cikinsa ta yi allawadai da yadda jami'an tsaro DR Congo sukayi amfani da karfi fiye da kima akan masu zanga-zanga da yunkurin tazarcen shugaba Joseh Kabila.
Rahoton wanda offishin MDD kan kare hakkin bil adawa a wannan kasa ta DR Congo wato (BCNDH) ya fitar a wannan rana ya ce, tsakanin ranakun 15 zuwa 31 na watan Disamba bara, akalla mutane 40 ne suka mutu kana wasu 147 suka raunana.
Haka kuma rahoron ya ce a lokacin an kuma jami'an tsaro sun tsare mutane 917 wadanda galibi ke zanga zanga lumana kamar yadda doka ta tanada.
Rahoton ya ce jami'an tsaron wadanda suka hada da sojoji da 'yan sanda da kuma masu gadin fadar shugaban kasa sunyi amfani da karfi da kuma harsashen bindiga wajen murkushe masu zanga zanga saboda rashin sani aiki da kuma horo akan tafiyar da masu zanga zanga, ba tare da hukumomin kasar ba sunyi wani abu ba ko kuma hukunta su ba.
Masu zanga-zanga dai na kyammar yunkurin tazarcen shugaba Kabila wanda wa'addin mulkinsa ya kawo karshe a ranar 20 ga watan Disamba 2016.