Gwamnatin Afirka Ta Kudu Ta Tasa Kiyar Wasu 'Yan Najeriya Zuwa Gida
Mahukuntan kasar Afirka ta kudu sun ce sun fara daukar wani mataki na tasa keyar wasu 'yan kasashen ketare da aka samu da wasu laifuka a kasar zuwa kasashensu na haihuwa.
A cikin bayanin da ma'aikatar harkokin cikin gidan kasar Afirka ta kudu ta fitar kan wannan batu, ta bayyana cewa wannan mataki ya shafi 'yan kasashen waje ne da suke aikata wasu laifuka na musamman a kasar, adadin mutanen da aka iya tantancewa sun kai daruruwa, kuma tuni aka fara tura wasu zuwa kasashensu.
Daga cikin wadanda aka koro dai har da wasu 'yan najeriya 97, bisa zarginsu da aikata laifuka daban-daban da suka sabawa dokar Afirka ta kudu, daga ciki kuwa har da wasu da suke mu'amala da muggan kwayoyi.
Sai dai ma'aikatar harkokin cikin gidan kasar Afirka ta kudu ta ce daukar wannan mataki ba shi da wata alaka da batun kyamar baki da wasu 'yan kasar suke nuna wa wasu 'yan kasashen ketare.