An kashe 'yan ta'adda biyu a tsakiyar kasar Tunusiya
Ma'aikatar tsaron Tunusiya ta sanar da kisan 'yan ta'adda biyu a tsakiyar kasar
Kamfanin dillancin labaran kasar Faransa ya nakalto Ma'aikatar tsaron Tsaron Tunusiya a jiya Laraba na cewa a ci gaba da farmakin da Dakarun tsaron kasar ke kaiwa tsibirin Kasrin domin tsarkake shi daga 'yan ta'adda da kuma masu tsatsauran ra'ayi, sun samu nasarar hallaka 'yan ta'adda guda biyu .Sanarwar ta kara da cewa ana ci gaba da kai farmaki a tsibirin na Kasrin har sai an tsarkake shi daga 'yan ta'adda.
Sama da shekaru biyar kenan da kasar ta Tunusiya ke fama da matsalar 'yan ta'adda a tsibiran kasar musaman a tsbirin Kasrin dake kusa da kan iyakar kasar da Algeriya, kuma mafi yawa daga cikin su 'yan kungiyar Alka'ida da ISIS ne inda suke mayar da tsibirin wurin buya.
Tun bayan tashin Al'ummar kasar ne a shekarar 2011 , 'yan ta'addar suka tsanata aiyukan su a kasar inda suka kashe jami'an 'yan sanda da Sojoji da dama tare da 'yan kasashen waje da suka shiga cikin kasar domin shakatawa kimanin 59.