Shugaban Gambia Na Ziyararsa Ta Farko A Senegal
Mar 02, 2017 07:42 UTC
Yau Alhamis, shugaban kasar Gambia Adama Barrow, ke fara wata ziyarar aiki a birnin Dakar na kasar Senegal.
Wannan dai ita ziyararsa ta farko a matsayinsa na shugaban kasar ta Gambia.
A yayin ziyara tasa Mista Barrow, zai gana da takwaransa na Senegal Macky Sall inda kuma zasu jagoranci wani taron manema labarai.
Ana kuma sa ran bangarorin biyu zasu sanya hannu kan yarjejeniyoyi da dama da suka shafi tattalin arziki da kuma diflomasiyya.
Tun da farko dai Adama Barrow ya yi ratsuwar kama aiki a offishin jakadancin kasarsa dake Senegal sakamakon kin mika masa mulki da tsohon shugaba Jammey ya yi.
Tags