D R Congo : Felix Tshisekedi Ya Zama Jagoran 'Yan Adawa
Mar 03, 2017 06:44 UTC
'Yan hammaya a Jamhuriya demokuraddiyar Congo sun zami Felix Tshisekedi a matsayin jagoran jam'iyyun adawa na kasar.
Mista Tshisekedishi kadai ne ya tsaya takara a matsayin mai nemen wannan matsayin, inda kuma aka zabe shi da gagarimin rinjaye.
kafin zabensa a wannan matsayin gamayar jam'iyyun adawa na kasar ta Congo sun kuma mika sunansa a matsayin wanda suke so ya zama fira ministan kasar a cikin shirin aiwatar da yarjejeniyar da aka cimma da gwamnatin kasar, bayan tazarcen shugaba Joseh kabila.
Felix Tshisekedi ya kasance da ga tsohon jagoran 'yan adawa na kasar Etienne Tshisekedi wanda ya rasu a ranar 1 ga watan Fabrairun daya gabata.
Tags