An Gano Daliban Jami'a Na Bogi 47,000 A Guinea
Ma'aikatar Ilimi mai zurfi a kasar Guinea ta ce ta gano daliban bogi sama 47,000 dake karatu a jami'o'in kasar.
Rahoton da ma'aikatar ta fitar ya ce an gano daliban ne a cikin jami'o'in gwamnati da kuma masu zamen kansu, sakamakon tsarin nan gwamnatin kasar na tantance daliban jami'a a duk fadin kasar.
Binciken ya ce a Conakry babban birnin kasar inda ake da daliban jami'a 52, 000, an gano cewa 19,000 ne kawai ke bisa ka'ida, inda sama da 32,000 na bogi ne.
A cewar ministan ilimi na kasar Abdoulaye Yéro Baldé, binciken zai baiwa gwamnatin kasar tattalin kudade da yawan su ya kai Bilyan 200 ne CFA a ko wace shekara, wanda kuma za'a amfana dasu wajen ingantawa da kuma samar da kayan aiki ga makarantun jami'o'in.