Wasu 'yan bindiga sun hallaka Mutane 3 a Burkina Faso
(last modified Sat, 04 Mar 2017 17:43:38 GMT )
Mar 04, 2017 17:43 UTC
  • Wasu 'yan bindiga sun hallaka Mutane 3 a Burkina Faso

Wasu 'yan bindiga sun hallaka Mutane uku a arewacin kasar Burkina Faso

Rahotanni dake fitowa daga birnin Wagadugu na kasar Burkina Faso na cewa wasu mahara da ba a kai ga tattance ko su waye ba sun kai hari a kauyen Kourfayel na jihar Soum dake arewacin kasar mai nisan kilomita 7 da kan iyakar kasar da Mali.

Jami'an tsaron kasar sun bayyana cewa Sojoji sun bi bayan maharan, amma ba su samu nasarar cabke su ba ganin cewa sun tsere cikin kasar Mali, ya zuwa yanzu babu wata kungiya da ta dauki alhakin kai harin, saidai kafafen yada Labaran kasar na dangata shi ne da kungiyar ta'addancin nan ta Ansarudin dake cikin kasar Mali.

Kasar Burkina Faso dai nada iyaka da kasashen Aljeriya Niger, Mali da kuma Guinee, kuma ta kwashe tsahon lokaci tana fama da hare-haren ta'addanci musaman ma a kan iyakokin kasar.

Tun bayan fara rikicin kasar Mali, kasashen dake makobtaka da ita irin su Jumhoriyar Niger da Burkina Faso  suke fama da hare-haren ta'addanci, inda ko a makun jiya sai da wasu mahara da ake kyautata zaton sun fito ne daga cikin kasar ta Mali suka kaiwa Sojojin Nijer hari a wani karamin gari dake kan iyakar kasar da Mali tare da kashe Sojojin kasar Akalla 15.