Ambaliyar Ruwa Ta Kashe Mutane 200 A Zimbabuwe
Mar 05, 2017 07:48 UTC
A Zimbabuwe mutane sama da 200 ne suka rayukansu sakamakon ambaliyar ruwa.
Rahotannin daga kasar sun ce tun a watan Disamba bara ne ruwa sama tamakar da bakin kwarya suka aukawa yankunan gabashi da kudancin kasar.
Ambaliyar ruwan dai ta raba mutane 2,000 da gidanjensu da kuma haddasa barna mai yawa, data shafi hanyoyi, gadoji da kuma awan gaba da dabbobi.
Hukumomin kasar dai sune ce suna bukatar tallafin Dala Miliyan 100 domin tunkarar wannan iftila'in, saidai tuni aka fara sukan gwamnatin kasar akan yadda ta ware makuden kudade wajen bikin zagayowar ranar haihuwar shugaban kasar Robert Mugabe a daidai lokacin da al'umma kasar ke cikin wannan bala'in.
Tags