'Yan Tawayen SPLM Sun Saki Mutane 125
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i18268-'yan_tawayen_splm_sun_saki_mutane_125
'Yan tawayen SPLA a Sudan sun saki fursunoni 125 da suka tsare kusan shekaru bakwai.
(last modified 2018-08-22T06:59:46+00:00 )
Mar 06, 2017 02:23 UTC
  • 'Yan Tawayen SPLM Sun Saki Mutane 125

'Yan tawayen SPLA a Sudan sun saki fursunoni 125 da suka tsare kusan shekaru bakwai.

Fursunonin da suka hada da sojoji 107 da kuma wasu fararen hula 18 an sake su ne a karkashin shiga tsakanin kungiyar agaji ta red croos.

Tuni dai mahukuntan kasar ta Sudan, suka yi maraba da sakin mutanen, wadanda a baya ke tsare a hannun 'yan tawayen a arewacin kasar.

Kungiyar 'yan tawayen SPLM dai ta saki mutanen ne a ranar Lahadi, tuni kuma suka isa birnin Khartoum fadar mulkin Sudan, inda suka hadu da iyalan su.

Da yake jinjinawa wannan mataki na kungiyar SPLM, ministan watsa labarai a Sudan Ahmed Bilal Osman, ya ce gwamnatin kasar ta yi matukar maraba da wannan mataki.

Tun cikin shekarar 2011 ne dai kungiyar SPLM ta fara fito na fito da gwamnatin Sudan a jahohin Blue Nile da kudancin Kordofan.