Somaliya: Yunwa Ta Kashe Mutane 110 A Cikin Sa'oi 48
Kamfanin Dillancin Labarun ( AFP) ya nakalto Pira ministan Somaliya na sanar da mutuwar mutane 110 saboda yunwa.
Pira ministan kasar ta Somaliya Khairi da ya fitar da bayani a ranar asabar ya fadi cewa; Mutanen da su ka mutu sun rika yin gudawa mai tsanani, a yankin kudancin kasar.
Pira ministan ya ci gaba da cewa; Wajibi ne ga mutane kasar ta Somaliya a duk inda su ke da su taimakawa 'yan'uwansu 'yan kasar mabukata da su ke fama da yunwa.
Har ila yau, pira ministan ya ci gaba da cewa; Aikin da ke gaban hukuma shi ne taimakawa mutanen da fama da yunwar, saboda farin da kasar ta ke fama da shi.
A yankin al-Bay na kasar mahukunta sun sanar da mutuwar mutane 69 mafi yawancinsu kananan yara da tsofaffi.
Tun a karshen watan Febrairu ne dai gwamnatin kasar ta Somaliya ta sanar da halin ko ta kwana saboda fari mai hatsari da kasar ta ke fama da shi.
Mutane miliya 3 ne dai farin ya jefa cikin yunwa kamar yadda kungiyoyin fararen hula su ka ambata.