Zimbabwe : Likitoci Sun Dakatar Da Yajin Aiki Don Tausayawa Jama'a
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i18278-zimbabwe_likitoci_sun_dakatar_da_yajin_aiki_don_tausayawa_jama'a
Kungiyar likitoci a Zimbabwe ta sanar da dakatar da yajin aikin data tsunduma yau kusa da makwani uku.
(last modified 2018-08-22T06:59:46+00:00 )
Mar 06, 2017 11:24 UTC
  • Zimbabwe : Likitoci Sun Dakatar Da Yajin Aiki Don Tausayawa Jama'a

Kungiyar likitoci a Zimbabwe ta sanar da dakatar da yajin aikin data tsunduma yau kusa da makwani uku.

Shugaban kungiyar ya shaidawa kanfanin dilancin labaren AFP cewa sun dakatar da yakin aikin don tausayawa jama'a, kuma tuni suka koma bakin aikinsu yau Litini.

Yajin aikin da likitocin suka tsunduma ya jefa rayuwar masara lafiya cikin muyuyacin hali, hakan ne yasa likitocin suka tausaya suka dakatar da yajin aikin duk da cewa tattaunawar da sukeyi da gwamnati ta cutura.

A watan Fabrairu daya gabata ne likitocin suka shiga yajin aikin domin cilastawa gwamnatin kasar biya masu wasu jerin bukatocinsu da suka hada da karin albashi da kuma inganta yanayin aikinsu.

Sha'anin kiwan lafiya al'umma na ci gaba da fuskantar koma baya kamar sauren bangarorin ma'aikatun gwamnati a Zimbabwe, sakamakon tabarbarewar tattalin arzikin kasar.