Sudan: An Bukaci Neman Gudanar Da Bincike Akan Harin Makamai Masu Guba.
Majalisar Dinkin Duniya ta yi kira da a gudanar da bincike akan harin makamai masu guba a yankin Darfur.
Majalisar Dinkin Duniya ta yi kira da a gudanar da bincike akan harin makamai masu guba a yankin Darfur.
Wani jami'in majalisar dinkin duniya, Micheal Margary ya yi ishara da harin na dabbanci da aka kai a yankin na Darfur, tare da cewa;" Rashin ghudanar da binciken bin kunya ne ga majalisar dinkin duniya."
A cikin watan Satumba da ya wuce ne majalisar dinkin duniyar ta gudanar da bincike da ya tabbatar da cewa sojojin gwamnati sun yi amfani da makamai masu guba a harin da su ka kai a Jabalu Murrah a yankin na Darfur.
Binciken ya kuma tabbatar da cewa mutane 200-250 ne su ka rasa raukansu sanadiyyar harin.