Burkina Faso Ta Hana Zirga-zirga A Kan Iyakarta Da Mali
Kasar Burkina Faso wace ta fuskanci hare-haren ta'addanci a baya bayan nan ta haramta zirga-zirga duk ababen hawa da dare a yankunan dake a kan iyakarta da kasar Mali.
Da yake bayyana hakan gwamnan yankin Kanal Hyacinthe Yoda, ya ce an haramta duk wata zirga zirga ta ababen hawa daga karfe biyar na yamma har zuwa shida na safe.
Matakin dai ya shafi ababen hawa da suka da mota, babur mai kafa biyu, da mai kafa uku da akafi sani da a daidaita sahu da kuma keke.
Motocin daukar marasa lafiya dake da takardar izinin yin aiki ne kawai keda hurumin yin zirga-zirga a yankin.
A kwanan nan dai hukumomi a Burkina faso na daukan matakai iri daban-daban na yaki da mayakan jihadi dake zamen babbar barazana a yankin.
Idan ana tune a watan Disamba bara sojojin Burkina faso 12 ne suka rasa rayukansu a wani hari da kungiyar Ansarul Islam ta dauki alhakin kaiwa a yankin Nasumbu.