Wani Babban Kwamandan 'Yan Ta'adda Na Alshabab Ya Mika Kansa A Somalia
Daya daga cikin manyan kwamandojin kungiyar 'yan ta'addan wahabiyyah takfiriyyah na Al-shabab ya mika kansa ga jami'an tsaron kasar Somalia.
Majiyoyin rundunar sojin kasar Somalia sun sanar da cewa, tun a jiya ne Hussain Salad Mukhtar daya daga cikin kwamandojin kungiyar Al-shabab ya mika kansa da makaman da ke hannunsa.
Wannan kuwa na zuwa ne bayan sanarwar da sabon shugaban kasar ta Somalia ya bayar, da ke cewa zai yi afuwa ga duk wani dan kungiyar Al-shabab da ya tuba kuma ya mika kansa da makamansa ga jami'an tsaro.
Kungiyar Alshabab wadda ke dauke da akidar takfiriyyah, ta sanar da yin mubaya'a ga kungiyar ISIS (Daesh) da ke da'awar jihadi domin kafa daular muslunci, kungiyar ta Al-shabab dai ta kashe mutane da dama a kasar Somalia da suka hada da jami'an gwamnati da kuma fararen hula a sassa daban-daban na kasar.