A Yau Ne Ake Sa Ran Shugaba Buhari Zai koma Nijeriya
(last modified Fri, 10 Mar 2017 05:46:29 GMT )
Mar 10, 2017 05:46 UTC
  • A Yau Ne Ake Sa Ran Shugaba Buhari Zai koma Nijeriya

A wani lokaci a yau din nan Juma'a ne ake sa ran shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari zai koma gida Nijeriya bayan hutu da kuma jinyan da yayi a birnin London na sama da wata guda.

Mai ba wa shugaba Buharin shawara kan harkar yada labarai, Femi Adesina ne ya bayyana hakan a yammacin jiya Alhamis cikin wata sanarwa da ya fitar inda ya ce a yau Juma'a ce shugaba Buharin zai koma gida bayan da likitocinsa suka amince da hakan.

Har ila yau sanarwar ta kara da cewa shugaba Muhammadu Buhari ya gode wa daukacin al'ummar Nijeriya da ma na  waje saboda addu'o'in da suka rika yi masa na fatan alkhairi da kuma samun lafiya.

Tun a ranar 19 ga watan Janairu ne dai shugaba Buhari ya tafi birnin London don fara hutu na kwanaki goma tare da ganin likitocinsa bayan wata wasika da ya aikewa majalisar dokokin kasar yana mai sanar da su mika wa mataimakinsa Yemi Osinbanjo cikakken ikon zama mukaddashin shugaban kasa kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada, to sai dai bayan karewar kwanaki goman shugaban ya sake tsawaita hutun nasa bayan da likitoci suka ba shi shawara ya tsaya ya ga sakamakon wasu gwaje-gwaje da aka yi masa.

Wannan tafiya ta shugaba Buharin dai ta janyo kace-nace a kasar musamman rashin gani ko jin muryarsa duk kuwa da ganawar da ya dinga yi da wasu masu fadi a ji a kasar da kuma wasu hotuna da ke nuna halin da shugaban yake ciki, lamarin da ya janyo magoya bayansa ci gaba da shirya tarurrukan addu'oin nema masa lafiya kamar yadda masu adawa da shi kuma suke ta yada labarurruka marasa dadi dangane da shi din.