Kokarin Najeria Na Daukan Bashi Domin Cike Gibin Kasafin Kudin Bana
Gwamnatin Najeria Na Kokarin daukan Bashi A Bankunan Duniya Domin Cike gibin Kudun kasafin Bana.
Kamfanin dillancin Labaran kasar Faransa ya Habarta cewa a yau Talata,Gwamnatin Najeria ta bukaci bashi daga bankin Duniya, Bankin bunkasa tattalin Arzikin Afirka da masu bayar da bashi domin cike gibin kudin kasafin kudin Bana.
Rahoton ya ce magabatan na Najeria na bukatar $ miliyar 3 da million 500 domin cike gibin kudin kasafin na bana.
Faduwar farashin Danyan Man A Duniya shine ya janyo Najeria shiga cikin wannan mawuyacin hali, domin kashi 90% na kudin shiga na kasar ya dogare ne kacoko kan Man fetur.
Mista David Yetes mai magana da yawun Bankin Duniya ya ce a halin yanzu suna cikin tattaunawa da gwamnatin Najeria dangane da siyasar bunkasa tattalin arzikin kasar kuma shawarwarin da magabatan Najeria suka bayar , shugabanin bankin duniyar za su gudanar da bincike kanta
A bangare guda kuma ,Bankin Bunkasa tattalin Arzikin Afirka ya sanar da cewa a Makun da ya gabata jami'ansa sun tattauna da magabatan birnin Abuja, bayan da Najerian ta bukaci bashin $ biliyan guda daga gare shi.