Gwamnatin Kenya Ta Jaddada Shirin Karfafa Matakan Tsaro A Yankin Arewacin Kasar
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i18420-gwamnatin_kenya_ta_jaddada_shirin_karfafa_matakan_tsaro_a_yankin_arewacin_kasar
Gwamnatin Kenya ta sanar da shirin karfafa matakan tsaro a kan iyakokin kasar da suke shiyar arewa sakamakon bullar abin da ta kira ayyukan wuce gona da iri da suke kara habaka a yankin.
(last modified 2018-08-22T06:59:48+00:00 )
Mar 11, 2017 08:37 UTC
  • Gwamnatin Kenya Ta Jaddada Shirin Karfafa Matakan Tsaro A Yankin Arewacin Kasar

Gwamnatin Kenya ta sanar da shirin karfafa matakan tsaro a kan iyakokin kasar da suke shiyar arewa sakamakon bullar abin da ta kira ayyukan wuce gona da iri da suke kara habaka a yankin.

A taron manema labarai da ministan harkokin cikin gidan kasar Kenya Joseph Nkaissery ya gudanar a birnin Nairobi fadar mulkin kasar ya bayyana cewa: Sakamakon tashe-tashen hankulan da suka faru a kan iyakokin kasar da suke shiyar arewaci a makon da ya gabata; Gwamnatin Kenya zata karfafa matakan tsaro a yankunan da nufin shawo kan duk wata matsala da ta shafi tsaron kasa.

Joseph Nkaissery ya kara da cewa: Gwamnatin Kenya ba zata taba zuba ido tana ganin wasu gungun 'yan daba da zauna gari banza suna kadamar da hare-haren wuce gona da iri kan jama'a ba, musamman gudanar da sace-sace da wawushe dukiyar jama'a, inda a wasu lokuta ake kai ga aiwatar da kisan gilla kan fararen hula.

Rikici da tashe-tashen hankula a yankunan da suke kan iyakokin shiyar arewacin kasar Kenya suna kunno kai ne a wasu lokuta da sunan rikicin kabilanci, inda suke lashe rayukan jama'a tare da barnata dukiyoyin jama'a.